Wata kotun shari’ar muslunci dake Zamanta a rijiyar lemo karkashin Mai shari’a Abdu Abdullahi wayya, ta yakewa wani matashi Mai suna Munzali Lawan, mazaunin unguwar kurna, Hukuncin kwashe kwata a unguwar Gwammaja Layin Azara tare da zuwa gaban Limamin masallacin juma’a na kurna, ya sauke Littafin kawa’idi.
Kotun ta yankewa matashin Hukuncin ne sakamakon samun da laifin Satar fitilar kan titi dakuma ta’ammuli da sholisho, Wanda hakan yasaba da Dokar final court dakuma sa sahi na 201 na dokar CGL.
Inda kuma a kotun dai aka yankewa wani matashi Mai suna Aliyu Naziru Hukuncin Haddar Izifi goma na Alkur’ani a makarantar Madarasatul Qira’atul Qur’an dake unguwar Gwammaja Layin Musa UAC, sakamakon samun sa da laifin shiga wani gida tare da kokarin haikewa wata yarinya Mai shekaru 17 da Haihuwa.