Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Matashin mai horar da wasan kwallon kafa da ya ja kungiyar Ramcy dake gidan sarki a birnin kano Bashir Isyaku Yakasai wanda akafi sani da Coach (Lemmy Adede) ya lashe kyautar gwarzon mai horarwa a gasar Rijiyar Ahlan Cup ta shekara ta 2022 da aka kammala,

Adede wanda ya karbi kyautar gwarzo mai horarwar gaban shugabannin hukumar kwallon kafa ta kasa NFF a wasan kashe da aka buga a ranar lahadin makon daya gabata a unguwar Rijiyar Zaki dake yankin karamar hukumar Ungogo ya zarta takwarorinsa da sukaja ragamar gasar wajen iya tsara kungiyar da koyar da wasa mai gamsar da yan kallon, Da’a da kyakykyawar shiga yayin kowane wasa,

Lemmy Adede wanda ke jagorancin kungiyar Danburan FC ta Daura dake jihar katsina a halin yanzu yayi zarra wajen jagorancin kungiyyoyi tare da samun nasara a matakai daban daban a tarhinsa,

Tsohon Kocin Good Hope , Samba Kurna, Malunfashi United, Rarara fc ya sha gwagwarmaya tare da samar da mafita ga kungiyoyi kwallon kafa a jihar kano dama wasu jihohi a arewacin najetiya a matakai daban daban

A tattaunawarsa da wakilinmu Adede ya godewa mabiyansa a fagen wasan bisa yadda suke mara masa baya tare da yabawa yan wasansa da shugabannin kungiyoyin da yake jagoranta bisa managarcin kokari da suke na amincewa da tsare tsaren da yake gabatarwa,

A jabinsa yayin bada kyautar shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano Sharu Rabiu Ahlan yabawa kocin Adede yayi bisa yadda ya rike aikinsa da gaskiya, abin da yace shine kashin bayan nasarori da Kocin ke samu, inda shugaban hukumar kwallon kafar ta jihar kano kuma shugaban kwamitin alkalancin wasa na kasa sharu ahlan din ke cewa ” Muna alfahari da irinsu Badhir Lemmy Adede ”

Daganan sai ya ja jankalin takwarorinsa da suyi koyi da shi,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *