Tsohon kwamishinan kananan hukumomin kuma Dan takarar mataimakin Gwamnan Kano a Jam’iyyar APC Hon. Murtala Sule Garo ya kaddamar da Shugabanin kungiyar Gawuna Garo promotion directorate guda 23 a matakin jaha.
Da yake kaddamar da Shugabanin Hon Murtala Sule Garo wanda ya samu wakilcin tsohon Shugaban karamar hukumar Nasarawa Hon Lamin Sani Kawaji yace wannan kungiya ta kasance ta farko a jirin kungiyoyin siyasa da suka fara yunkurowa domin ganin sun fito da manufofin yan takarar Jam’iyyar APC a jahar kano.
A nasa jawabin Shugaban kungiyar Gawuna Garo promotion directorate Hon Aminu Musa Jijitar kuma mataimakin shugaban karamar hukumar Gabasawa ya bayyana jin dadinsa bisa yadda suka sami damar kafa wannan kungiya cikin nasara tare da bayyana manufofin da suke da burin cimma a kungiyar.
Taron wanda ya gudana a ofisoshin kungiyar ta Gawuna Garo promotion directorate dake shataletalen Dangi dake kan titin zaria ya samu hartar mutane da dama ciki har Shugaban karamar hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban Kauye da takwatansa na karamar hukumar Takai Hon Baffa Takai dadai sauransu.