Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Yayin da ya rage sa’oi kadan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta rufe rijistar zabe, yanzu haka dubban alumma sunyi dafifi a ofisoshin hukumar dake kananan hukumomi a Kano.
Kamar yadda muka sani damar zantawa da wasu daga cikin mutanen sun bayyana damuwarsu kan wannan batun na rufe yin rijistar inda sukace kamata yayi ace hukumar ta kara wa’adin makonni hudu zuwa shida ta yadda zasu samu damar mallakar katin zaben.
Saidai a gefe guda kuma wasu sun bayyana cewar sunje ofishin hukumar ne tun da asubahin fari amma har lokacin da suke bayanin da misalin karfe 7:40 na dare basu samu damar yin rijistar ba, wanda sukace abin ya zama sai wanda suke da farcen susa.
Haka zalika, wani daga cikin ma’aikatan da muka samu damar jin tabakinsa wanda ya nemi a sakaye sunansa, yace suna iya bakin kokarinsu domin ganin sunyiwa mutane rijistar amma rashin wadatattun kayan aiki shine abinda yake dakile yunkurin nasu inda ya koka da cewar a hukumancema naira dubu daya ake basu a matsayin kudin da zasu zuba mai a injin da zasuyi aikin wuni guda dashi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *