An sauyawa dakin Kaaba sabuwar riga wato Kiswah, da aka kashe dala miliyan 6.5 wajen ɗinkata a safiyar wannan Asabar din.
An soma aikin sauya rigar tun daren Juma’a bayan Sallar Isha’i aka zuwa asubahin Asabar, wanda ya zo daidai da ranar 1 ga watan Muharram 1444 A.H.
An kiyasata cewa nauyin sabuwar rigar ya kai kilogram 850, kuma a yanzu ya kasance irin wannan riga mafi tsada a duniya.
Wannan shi ne karon farko da ake sauya Kiswah wato kamar yada ake kiran rigar, a ranar 1 ga watan Muharram.
Kafin wannan lokaci ana sauyawa Kaaba rigar ne a lokacin aikin Hajji, musamman a safiyar 9 ga watan Dhul Hijjah idan alhazai sun tafi hawan Arafa.
Karkashin jagorancin Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais da ke kula da manyan masallatai biyu mafi daraja a duniya, ya ce an sauya lokacin sauya rigar Kaaba ne bisa sabbin dokoki da shawarwari masarautar Saudiyya.
Mutane sama da 200 ne dai kafofin yada labarai ke cewa suka yi aiki akan rigar Kaaba daga wajen dinkata har zuwa ta sanyata a jikin Kaaba.