A cigaba da sauraren shari’ar Sheak Abduljabar kabara da Gwamnatin Kano, a zaman kotun na yau kotun ta tintibi Lauyan Gwamnati Suraja Sa’ida SAN kan ko me zaice dangane da rokon da wanda ake Kara yayi naneman a chanza masa kotun, inda Layan yai suka kan haka.
Bayan da kotun ta juya ga Lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma Barista Dalhatu Shehu Usman yace Yana bukatar kotu tabashi lokaci domin yin nazari kafin yace wani abu. Inda take kotun ta bashi mako guda domin yazo ya gabatar da nasa martanin.
Daga karshe Alkhalin kotun mai shari’ Ibrahim Sarki Yola ya dage cigaba da sauraren karar zuwa Ranar 4 ga watan Augusta 2022.