A yau ne Wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a birnin tarayya Abuja ta bada belin dakataccen akanta kaneral na gwamnatin tarayya Ahmad Idris da kuma mutane biyu da ake zargin su tare wanda hukumar da ta ke yaƙi da hana cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ke tuhumar su.
Alƙalin kotun mai Shari’a Adeyemi Ajayi ya gindaya musu sharaɗin kar su bar birnin tarayya Abuja sakamakon za a iya neman su kowanne lokaci.
Kazalika idan suna son barin tarayya Abuja sai sun nemi izini daga kotun ,idan kuma suka saɓa haka sun karya sharuɗan belin .
A ƙarshe kuma kotun ta basu takaddar rantsuwa tare da saka hannu kamar yadda EFCC ta buƙata.