Rahotanni sun ce shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal yaki amincewa da bukatar tattauna tsige shugaban kasar, sai dai mahawara akan yadda matsalar tayi kamari da kuma baiwa shugaban kasar wa’adi domin shawo kan su, idan kuma ya gaza sai akai ga bukatar tsige shi.
Bayanai sun ce hana tattauna bukatar tsige shugaban kasar da Lawal yayi ta sanya wasu ‘yan majalisar sama da 10 haure takalaman su domin ficewa daga zauren majalisar.
Kamar yadda rahotanni ke cewa, yunkurin janyo hankalin shugaban majalisar da shugaban marasa rinjaye Sanata Philip Aduda yayi, bayan sun kwashe sa’oi 2 suna tafka mahawara a asirce, yaci tura.
A wannan mako, Yan bindigar sun kashe sojoji guda 3 a Abuja, babban birnin kasar da kuma kai hari kusa da kwalejin gwamnati dake Kwali, abinda ya tilasta rufe makarantar.
Bayan ficewar ‘yan adawar, majalisar ta baiwa shugaba Buhari wa’adin makonni shida da ya magance matsalar tsaron, ko kuma ya fuskanci tsigewar.