Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar dogarawan fadar shugaban kasar ta ce ta baza jami’anta a kewaye da dazukan Bwari domin fatatakar ƴan bindigar da suka yi wa jami’anta kwantan-ɓauna a daren ranar Lahadi.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce an murƙushe harin da aka kai musu na ranar Lahadi, sai dai akwai jami’anta da dama da suka jikkata.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da wasu kafofin yaɗa labarai a Kasar nan ke cewa sojoji uku sun rasa rayukansu a harin, ciki harda wani kyaftin.

Harin na daren Lahadi ya auku ne kan sojojin da ke bayar da tsaro a kewayen kwalejin koyar da aikin lauya da ke Bwari a birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Bayan kwalejin ta aike da saƙon ankarar da jami’an tsaro kan wata wasikar barazanar kai musu hari da aka kai wa makarantar.

Rahotanni kamar yada wasu kafofin yada labarai  suka fitar na cewa wadanda aka kashe sun hada da wani Kyeftin din soja guda da kuma wasu sojoji biyu da ke aiki da rundunar dogarawar fadar shugaban kasa.

Kafin a hallaka su, sai da suka je makarantar suka tattauna da mahukunta kan matakan da ya kamata a dauka domin kare dalibai da malamai da ginin makarantar.

Sai dai kamar yadda masu Magana ke cewa baya bata da kaɗan, bayan barin kwalajen a hanyar da ta haɗa Bwari zuwa Kubwa, sai ƴan bindigar suka yi musu kwanton-ɓauna, nan take kuma sojojin uku suka kwanta dama.

Sai dai kakakin rundunar dogarawan fadar shugaban ƙasa, Kyeftin Godgrey Anebi Abakpa, da ke tabbatarwa da BBC harin a wata sanarwar da ya aike, ya ce an jikkata jami’ansu da dama da yanzu haka ke samun kulawa a asibiti. Kuma kawo yanzu suna tattara bayanai don haka ba za su iya fayyace kashe sojojinsu ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *