Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Dakarun Operation Hadin Kai, sun tabbatar da kubutar da wata ‘yar makarantar Chibok, Ruth Bitrus da ta kubuta daga hannun ‘yan Boko Haram da yaronta.

Kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar GC Musa ne ya bayyana haka a Barikin Maimalarin a lokacin bikin mika kayan aikin jinya da hukumar raya arewa maso gabas ta yi domin tallafa wa sojoji a ranar Laraba.

“Za ku iya tunawa cewa a makonnin da suka gabata mun kubutar da ‘yan matan Chibok biyu da ‘ya’yansu, zan so in sanar da ku cewa mun kubutar da wata guda a yayin gudanar da ayyukanmu.

“Ba za mu huta ba har sai an dawo da Leah Shaibu da sauran ‘yan matan Chibok tare da hada kan iyalansu. Ba za mu huta ba har sai an dawo da su lafiya. An ceto Ruth Britus daga dajin Sambisa tare da danta,” inji Manjo Janar Musa.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne sojojin suka kubutar da ‘yan matan Chibok biyu Mary Dauda da Hauwa Joseph bayan sun tsere daga sansanin ‘yan Boko Haram da ke Gazuwa mai tazarar kilomita 9 zuwa karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *