Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta ce ta samu rahoton wasu tsofaffin mambobinta da suka koma jam’iyyar adawa ta PDP a jihar.
A cewar wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar na jihar, Kwamared Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ba ta sa ran sauya sheka ba.
Ya ce sun gaza sanar da jam’iyyar a hukumance matakin da suka dauka wanda ba don wani dalili ba ne illa kawai girman kai.