Gabanin zaben 2023, Reno Omokri, wani mai fafutukar siyasa da zamantakewa, ya bayyana cewa Bola Tinubu, jam’iyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa ba barazana bane ga jam’iyyar PDP.
Omokri ya ce babbar barazana ga nasarar PDP a 2023 shine Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ba Tinubu ba.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Omokri, wanda na hannun damar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Tinubu, wanda ba zai iya tabbatar da nasarar APC a jihar Osun ba, ba zai iya kawo barazana ga nasarar PDP ba.