Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban cibiyar koyar da wasan kwallon kafa na Shugaba Business Solutin (SBS) dake jihar Lagos yasha alwashin bunkasa cigaban wasan kwallon kafa tsakanin matasa dake fadin kasa da arewacin najeriya musamman jihar Kano,

Da yake jawabi a wata tattaunawa ta musamman da yayi da wakilin express radio shugaban. Muhammad Bello Shugaba cewa yayi duk da cewa shi ba dan jihar kano bane, amma ya zabi jihar ta kano dan zama cibiyar horar da duk yan wasan da yake horarwa da turasu mataki na gaba,

Dayake amsa tambaya kan dalilinsa na zabin kano duk da cewa shi ba dan jihar bane Muhammad Bello Shugaba .cewa yayi ” Na dade ina harkokin wasan kwallon kafa amma a jihar Lagos kafin zuwansa kano a 2013 zuwa 2014 inda ya gano cewa akwai managartan yan wasa”

Bello Shugaba wanda yace ya dade yana harkokin amma zuwansa arewacin najeriya sai ya gane cewa ashe yan wasa masu nagarta na arewacin najeriya inda ya kara da cewa ” ina mamaki da masu neman yan wasa basa zuwa arewa”

Dangane da abin dayaja hankalinsa na shiga harkokin kwallon kafa Muhammad Bello Shugaba cewa yayi ” harkar kwallo ajinina take kuma harkace da ake samun arziki idan an daure, kuma anyita da gaskiya,

Shinko me kake nufi da anyi ta da gaskiya ? sai yace ” E na taba samun damuwa wacce banji dadinta ba saboda haduwa da nayi da marasa amana amma komai ya wuce” inji

Dangane da kalubalen daya fuskanta daga lokacin daya fara harkar kwallon kafa zuwa yanzu Shugaba cewa yayi akwai kalubale kamar yadda na gaya maka na haduwa da marasa gaskiya da amana cikin harkar abin da yakesa wasu irina masu son su taimaka suke guduwa daga harkar,

Dangane da abin daya ja hankalinsa na kafa kungiyar SBS cewa yayi ” nayi dacen samun abokan aiki masu gaskiya da irikon amana ya sanyani cigaba da daukar nauyin kungiyar kuma kawo iyanzu abubuwa suna tafiya kamar yadda ya kamata,

Kan yadda kungiyar ke gudanar da tsarin ta da manufofinta Muhammad Bello Shugaba cewa yayi akwai aji daban daban na rukuni da shekarun yan wasan har hawa hudu (4) akwai yan U-13, U-15 , U- 17 da kuma sama da haka wadanda muke turawa zuwa kungiyoyi daban daban, kuma kawo iyanzu muna da yan wasa da dama a kungiyyoyi na najeriya da suke buga league NPFL da dama,

Da yake amsa tambaya na cewa ko kai dillalin yan wasa ne ? sai Muhammad Bello yace “E ni Intermediary ne ” wato ma shiga tsakanin kungiyoyi dan cinikin yan wasa da tallatasu a matakai daban daban a ciki da wajen kasarnan,

Shinko ka taba fidda dan wasa zuwa kasar waje sai shugaban na SBS Academy yace ” Kwarai ina da yan wasa da dama a turai kuma duk sun sami kulab kuma suna kokari,

Inda ya kara da cewa na baya bayan nan shine ya je maldova inda yayi zaman wucin gadi daganan kuma ya wuce zuwa Isiraila inda yake taka mahimmiyar rawa a wasan league na kasar harma turawa ke bibiyar yadda yake taka Leda kuma suke kaunarsa.” kaunar da basaina fada makaba” inji Shugaba

Dangane da yadda yake kallon masu hali ke shiga harkokin wasan kwallon kafa Mohammad Bello cewa yayi “A gaskiya anbar yan arewacin najeriya a baya wajen sanya kudadensu a harkar wasan ko kan dan wasa inda yace a kudanci najeriya Iyaye da yan uwa ne suke zuba jarinsu kan Dan su da yake da basirar kwallo tare da goya masa baya, sabanin arewacin najeriya musamman kuma jihar kano jihar da Muhammad Bello ke cewa tafi kowace jiha yan wasa masu basira,

Dangane da yadda yakeyi da cibiyar SBS Shugaba cewa yayi ” Komai ana ni nakeyi tare da masu taimakawa awajen gudanar wa musamman Baba Alhaji da Abokina Yunusa Uba wanda team manager ne a kano pillars kuma aminina da saura wadanda muke gudanar da harkar,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *