Gwamnatin jihar Kano ta sanar da hana zirga-zirgar babura uku da aka fi sani da A Daidata Sahu daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe daga ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.
Wannan aiwatar da wannan mataki na daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar, inda ya tabbatar da cewa an cimma matsaya kan haramcin gudanar da ayyukan babur uku a cikin wa’adin da aka kayyade a karshen taron tsaron jihar.
Kwamishinan ya bukaci masu tuka keke masu uku da su bi su daina aiki a cikin sa’o’in da aka kayyade domin jami’an tsaro za su aiwatar da dokar ba tare da tsangwama ba.