Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Fadar shugaban kasa a daren jiya ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Katsina.

Fadar shugaban kasar ta kuma ce mutane biyu da suka samu raunuka sakamakon harin, suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.

A gobe Juma’a ne ake sa ran shugaba Buhari zai je Katsina, jiharsa domin gudanar da bikin Sallah.

Wata sanarwa da babban mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce: “Fadar shugaban kasa ta bayyana a matsayin abin bakin ciki da rashin jin dadi, lamarin da ya faru a kusa da garin Dutsinma a jihar Katsina, kan ayarin motocin da ke dauke da kungiyar Advance Team. jami’an tsaro, protocol da jami’an yada labarai gabanin tafiyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa Daura domin yin Sallah.

“Maharan sun bude wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton bauna, amma sojoji da ‘yan sanda da jami’an DSS da ke raka ayarin sun dakile.

“Mutane biyu da ke cikin ayarin motocin suna karbar magani kan kananan raunukan da suka samu.

“Dukkanin sauran ma’aikata, ma’aikata da motoci sun isa Daura lafiya.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *