Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban kamfanin Gadco Nigeria Limited Hassan Gaddar ya sha alwashi daukar nauyin wata kungiya mai suna Pop Cola dake Brigade a Karamar Hukumar Nasarawa bayan Nasarar da kungiyar ta samu da sunan kamfanin a gasar cin kofin kwallon kafa na Ramadan na shekara ta 2022 da aka sanyawa kungiyoyi sama da 30 a fadin karamar hukumar.

A bayyaninsa yayin wani kayataccen taro daya shiryawa tawagar kungiyar yayin da suka kaimasa ziyarar godiya da mika kofi a kamfaninsa dake Titin Tafawa Balewa a jihar kano, Hassan Gaddar ya yaba da kwazon yan wasan kungiyar bisa nasarar da suka samu tsakanin takwarorinsu sama da talatin (30) da suka shiga gasar,

Gaddar wanda yace lokaci yayi da zai dauki nauyin kungiyar laakari da yadda suka taka rawar gani a gasar ya zama wajibi kamfanin ya nuna musu jindadinsa da yadda suka fito da sunan kamfanin a fagen wasan kwallon kafa,

Shugaban ya kara da cewa wasan kwallon kafa shine abu Daya a duniya da yake hada kan Al’ umma ya ja hankalin yan wasan dasu maida hankali wajen Santa kwazo da kishin juna da ganin sun sami nasara a harkokin su,

Hassan Gaddar ya kara da yabawa dan uwansa Ahmed Tahir wanda yace ya bada gudunmawa sosai wajen ganin kamfanin ya shiga cikin harkokin wasanni musamman daukar nauyin gasar duk da irin halin matsin tattalin arziki da ake fuskanta, yace Ahmed Tahir zai zama madubi da sabuwar kungiyar zata dunga kallon da tuntuba a duk lokacin da suke bukatar wani abu,

Gaddar wanda cikin jin dadi da alfahari ya karbi tawagar yace ” Gaskiya kun burgeni, kuma zan dauki nauyin kungiyar saboda kuna amsa sunan Pop Cola”

” Zan cigaba da daukar nauyin kungiyar har sai ta zama abar alfahari a jihar kano” inji Hassan Gaddar

Daganan saiya godewa shugabannin kungiyar da yan wasa bisa yadda suka hada kansu da yin kokari har suka samu nasara, inda ya gargadesu dasu kaucewa shaye – shaye da harkokin da basu kamata ba, kana su zama jakadu na gari na kamfanin pop cola a ko’ ina.

Taron ya samu halartar daukacin yan wasa da shugabannin kungiyar da shugaban kwamitin shirya gasar da wasu daga cikin maaikatan kamfanin da suka shaida kasai taccen taron da aka gudanar

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *