Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Fitaccen jarumai kuma mai shirya fina finai a masana’antar Kannywood TY-Shaban yace yana fatan Shirin film din Andalu da Lulu wanda ya jagoranci shiryawa, ya zama zakaran gwajin dafi a wannan shekara ta 2022 bisa nagartaccen labari da kuma kwararru da aka dauka suka Jagoranci aikin film din.

TY Shaban yace ranar litinin 4/7/2022 zai saki tallan Shirin film din domin duniya miliyoyin mutane dake dakon kallon Shirin su fara ganewa idanunsu abinda Shirin film din ya kunsa.

TY Shaban na wannan jawabin ne a ranar Juma’a 1/7/2022 lokacin bikin kaddamar da tallan film din a matakin farko a gidan kallon zamani na Platinum Cinema dake kan titin Zaria a Kano.

Daruruwan masu shirya fina finan, marubuta, masu bada Umarni, jarumai, mawaka na arewaci da kudancin kasar nan, da kuma kwararru da Jan Jarida na daga cikin wadan suka halarci bikin kaddarlmar da tallan film din da aka gudanar jiya juma’a.

Shirin film din Lulu da Andalu zai taimaka wajan bun kasa masana’antar shirya fina finan Kannywood, wanda nan gaba kadan duniya zata kara gamsuwa da aiyukan Kannywood wanda hakan zaisa masana’antar ta fara karbar manyan lambobin yabo a mataki na Duniya, sakamakon fara daukar wani ingantacce kuma nagartaccen sabon shirin film mai dogon zango maisuna “Lulu da Andalu” wanda duk kanin abinda labarin ya kunsa abu ne da ya faru a zahiri.

MANSA MUSA wani shaharerren mai dukiya ne dan kasar MALI wanda tarihi ya tabbatar da cewa ya taba zama mutumin da babu wanda ya kaishi tarin dukiya a fadin duniya, yayi mulkinsa a matsayin MANSA na MALI tsakanin shekara ta 1312 sannan kuma ya rasu a shekara ta 1337.

Sai kuma kwatsam a wannan zamanin namu na shekara 2022 aka sami wani bawan Allah wanda burinsa shine ya gano inda dukiyar MANSA MUSA take domin ya mallaketa, sai dai kafin gano inda dukiyar MANSA MUSA take dole sai an taso da wasu hatsabiban Aljanu guda biyu wato LULU da ANDALU daga wani dogon barcinsu na shekaru sama da 700 da suka gabata suna shekar kayansu.

Haka kuma shirin film din zai nuna yadda dangantaka da mu’amular rayuwa ke gudana tsakanin bil’adama da ‘Jinnu” ke kasan cewa ta yadda mutum da aljanu zasuyi aiki tare wajan gano maboyar wani sirri na tarin dukiyar MANSA, inda bil’adama da jinnu za suyi amfani da tsafi wajan gudanar da aikinsu. Ko ta yaya hakan zai yuwu?? Wannan na daga cikin tarin tambayoyin da zuwa yanzu mutane keyi.

Domin tabbatar da yuwar wannan gagaramin aikin film, mashiryin shirin Lulu da Andalu TY Shaban ya dauki kwararrun masana aikin shirya film da jarumai maza da mata sama da dari hudu “400” domin tabbatar da ganin wannan gagarimin aiki ya tabbata kamar yadda ake da bukatar ya zama na musamman, wanda masana sukayi imanin zai gamsar da duniyar makallata fina finai na fadin Duniya.

Wannan wani abun yabawa ne bisa bijiro da wannan aiki duk kuwa da yanzu haka ana kan gudanar da aikin shirya wannan film din ne, shirin film din wanda kaso tamanin 80% cikin dari sabbin abubuwa ne na kir kira a cikinsa, wanda ke bukatar kwararru wajan aiwatar da shi, wannan ce tasa duk kanin jaruman dake taka rawa a cikin film din saida aka basu kwaryar kwaryan horo domin kara sanin makamar aiki yadda ya kamata.

Daga karshe dai muna fatan ganin wannan Gawurtaccen film daga masana’antar shirya fina finai ta Kannywood wanda zai gamsar da masu kallo na fadin Duniya, wanda kuma hakan zai janyo tafka ingantacciyar muhawara mai ma’ana a tsakanin jama’a.

Saboda haka mu jira fitowar wannan kayataccen shiri. Jin jina ga duk kanin masu ruwa da tsaki na shirin LULU DA ANDALU.

Musamman mashiryin Shirin Ty Shaban da Kamilu Dan Hausa Wanda ya bada Umarni da sauran zaka kuran maaikata da jaruman da suka taka rawa a Shirin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *