A yayin da aka bude kasuwar musayar tsoffin yan wasa tsakanin bangarorin dake jagorancin yan wasa na kano all stars gabanin tinkarar zagaye na biyu na gasar da aka fara yan watanni da suka gabata jagoran bangare daya daya sayi Salisu Yusif Zico a baya bayan nan Dr Danburan Abubakar yace ya zama wajibi ga kungiyar da yake jagoranta data sayi dan wasa zico daga hannun kungiyar Abba Galadima komai.tsadarsa , duba da cewa irin dan wasane da ” kungiyata ke bukata” da kuma kwarewarsa.
Dan gane da yadda akayi ciniki da kuma farashin dan wasan Dr Danburan yaki bayyana yadda kudin yake amma ya tabbatarwa da wakilinmu.cewa an kammala cinikin, kuma an biya harma wakilimu ya ruwaito mana cewa anga dan wasan tare da Dr Danburan din a lokacin da suke ganawa ta karshe na kammala batun sauya shekar kuma dan wasan ya tabbatarwa da wakilinmu cewa ” E gaskiyane ya sauya sheka xuwa tawagar Dr Danburan ” inda yace ” zanyi iya bakin kokarin ganin na bada gudummawa ga kungiyar dan samun nasarorin da ake bukata,
A karshe makon nan ne ake sa ran fara zagaye na biyu na gasar da ake bugawa tsakanin tsoffin yan wasan kwallon kafa na Vetrans All Stas na jihar kano ta shekarar 2022 da ake je hutu tare da bude kofar musaya