Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Bayan shafe makwanni biyu ana fafatawa tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a jihar kano a gasar cin kofin Hon Abba Muktar a.k.a Fifa Agent karon farko, sai gashi kungiyoyi da mabiya wasan kwallon kafa a jihar kano na cewa san barka,

Laakari da yadda aka tsara gasar da a wannan bangare ake ganin sabon abu na samar da riguna (Jersey set ) ga kowace kungiya da kwallo kyauta abin ya sauya salo da tunanin masu kungiyoyi da yan wasa da mabiya harkokin wasan a wannan nahiyi,

Amma ga masu bibiyar Abba Muktar da irin yadda yake hidimtawa yan wasa da kungiyoyi ba abin mamaki bane dan anga yadda ake bawa kungiyoyi kayan wasa a wannan gasar,

Rahotannin sun bayyana cewa ko a shekara ta 2007 a yakin karamar hukumar Nasarawa kimanin kungiyoyi 250 ne suka amfana da set na Jersey da Beefs da Kwallayye sama da 4000 da Abba Muktar din ya rabawa kungiyoyin kyauta dan bunkasa cigaban su,

A wata tattaunawa da wakilinmu.yayi da wasu masu kungiyoyi da yan wasa da suka shiga gasar sun bayyana masa cewa wannan shine karo na farko da suka shiga gasa irin wannan, kuma abin jin dadi shine “yadda jami’an gasar ke kyautata muamalla tsakaninsu damu masu kungiyoyi da yan wasanmu ” inji masu kungiyoyin,

Kyakykyawan tsarin da jagororin gasar sukayi shine yaja hankalin yan kallo daga ko ina a fadin jihar kano ciki kuwa harda wasu sassa na kananan hukumomi.kamar su Rimin Gado, Kumbotso, Ungogo, Tofa ,Dawakin Tofa ,Gezawa zuwa kallon wannan wasa harma suke kira da masu shirya gasar dasu sanya makamanciyar gasar a yankunan kananan hukumomin su,

Kawo iyanzu gasar cin kofin Abba Muktar Super Cup tayi tambarin da duk jihar kano ake mararin kallonta a duk mako inda sama da yan kallo 5000 ke kallon wasan a kowace rana

Abin jira a gani shine, shin ko wannan gasa zata zama gasar shekara shekara ko kuwa ?

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *