Kwallon da Dan Wasan Gaba na Gaida United ( A A. Zaura Babes )Halifa Umar Gaida ya sanya mintina 14 da fara wasan karshe na cin kafin Lola Cup karo na farko ne ya bawa kungiyar ta Gaida United nasarar lashe kofin karo na farko da sama da kulab 24 suka fafata,
Halifa Gaida dan wasa gaba ne da Allah ya bashi tsawo, karfi da kuzari, daya zama abin kallo da ambato ga wandanda suka kalli wasan karshen da aka buga a filin wasana .dake garin fanshekara,
A zantawarsa da express radio jin kadan bayan kammala wasan Halifa yace ” Nagode Allah daya bamu wannan nasara kuma naji dadi da ni nasanya kwallon data bawa kungiyata nasara”
Dan gane da yadda ya shiryawa wasan karshe Halifa cewa yayi ” Gaskiya na shiryawa wannan wasan dan har mafarkinsa na dingayi kuma gashi burina ya cika a kansa”
Dan gane da kungiyarsa ta Gaida United A A Zaura Babes Dan wasan cewa yayi ” goyon bayan da muke samu daga shugabancin kungiyar alamace ta cewa zamu cigaba da samun irin wannan nasara ”
Da yake bayani kan burinsa a wasan kwallon kafa Halifa cewa yayi inaso in cigaba na sami daukaka zuwa mataki na gaba da yardar Allah,