Bayan kimanin shekaru 3 zuwa 4 da barinsa wakilcin karamar hukumar birni a majalisar wakilai ta kasa Dr Danburan Abubakar Nuhu yakai ziyara makarantar Ulumuddeen dake Unguwar Sharada Gindin Garu daya daga cikin makarantu 5 daya gina lokacin ludayinsa na kan dawo,
Da yake jawabin makasudin ziyarar tsohon dan majalisar Dakta Danbiran Nuhu yace ” taaziyyar wani dattijo dake da alaka da makarantar ce ta kawoshi kuma yaga dacewar ya shiga dan ya duba makarantar”
Inda ya kara da cewa ” wannan dattijon daya rasu, Dattijo ne dana fara haduwa dashi kimanin shekaru 7 da suka gabata lokacin ina zagayen neman sahalewar mutanen karamar hukumar birni na wakilcin danayi kuma shi wannan Dattijo Marigayi ya gabatarmin da makarantar mukayi magana nace zan rusheta na gina sabuwa, kuma cikin ikon Allah hakan ta tabbata kuma shi wannan Dattijon daya rasu ya cigaba tabbatarwa da Duniya cewa yadda nayi alkawari kuma Allah ya bani Ikon cikawa ” Allah ya jikansa yasa aljannace makomarsa” inji Danburan
Dangane da yadda ya ziyarci makarantar daya Gina dan bunkasa Ilimin Addinin Musuluci Farin Jakada cewa yayi ” Nayi matukar farin ciki da yadda naga makarantar cikin tsafta da tsari kuma wannan makarantar abin alfaharice gareni saboda itace ta farko dana fara ginawa ina Dan Majalisa daku yadda makarantar ke tara dalibai daga gurare da dama da irin nasarorin data samu na yaye dalibai masu haddar Alkurani Maza da mata,
Dan gane da yadda yakeji bayan ganin abin daya gina da hannunsa na bunkasa wajen samar da managartan dalibai Danburan cewa yayi ” Wannan Shine irin ayyukan da tun kafin naje majalisa nake da burin yi kuma gashi Allah ya bani iko nayisu a fadin karamar hukumar birnin kano a gurare 5 inda suka hadarda na Sharada inda na kawo ziyara da Gandun Albasa,da Kankarofi da Zangon Bare bari da kuma Yakasai” dama burina bunkasa cigaban addinin musulunci ” Allah mungode”
Danburan ya cigaba da cewa”wadannan ayyukan na daga cikin cikar burina na samar da aiki mai dorewa da wanzuwa na addini da alumma zasu dade suna amfana,
Dan takarar sanatan kano ta tsakiya a yanzu Danburan Abubakar ya kara da godewa alummar mazabar sharada bisa irin girmamawa da sukayi masa lokacin daya kai wannan ziyarar taaziyya inda yace ” nayi farin ciki da ganin yadda kyakykywar alkarmu take da wadannan mutane da yadda suka karbeni duk da cewa babu wasu madafun iko a hannuna nagode Allah yabar zumunci.