Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wani gagarumin taro da mabiya darikar shekariyya na karamar hukumar Gwale suka gabatar dan neman mafita ga shugaban darikar Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau da sauran mabiyansa karkashin jagorancin Tsohon Walilin Karamar Hukumar a Majalisar Wakilai ta Kasa Honourable A A Sule Lokon Makera da aka gudanar a gidan sa dake kofar naisa ya goyi bayan ficewa daga jamiyyar APC ba tare da bata lokaci ba,

Da yake karanta wata takarda mai shafi sama da 5 da babban kwamitin Shura na tafiyar Malamin da aka aikewa kowace Karamar Hukuma tsohon kwamishina Sarki Labaran ya bayyana cewa an aika wakilai da makamanciyar wannan takarda ga kowace karamar hukuma wacce take dauke da cikakken bayanin abubuwan da suka faru tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Gwamnati da Shugabancin Jammiyyar APC na jihar Kano tun bayan samun Nasarar zaben 2019 tare da umartar magoya baya dasu zauna a ranar alhamis da misalin karfe biyu na rana a kowace karamar hukuma dan jin abin da takardar ta kunsa tare da fidda matsaya ka sadarar karshe na takardar wanda yace ” shin zama a jamiyyar zaayi ko ficewa ?” Ina Nagoya bayan tsohon gwamnan Malam Shekarau sukace a fice daga jamiyyar bayan da Hon A A Sule ya nemi jin raayinsu kamar yadda takardar ta bukata,

Wani bincike da wakilinmu Salisu Musa Jegus ya gudanar kan inda magoya bayan suka karkata, yayi nuni da cewa da dama daga cikinsu na shaawar tsallakawa sabuwar jamiyyar NNPP ta tsohon sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin da wasu kadan daga cikin ke cewa ayi hattara wajen komawa kowace jamiyya dan gujewa abin. daya faru a baya, inda wasu kuma ke shawartar Malamin da ya fara tunanin kafa jamiyyarsa da mutanensa dan samun makoma da tabbataccen tsari, dan kaucewa yadda yan siyasa ke amfani da malamin da magoya bayansa wajen cimma buri. inda kuma ake watsi dasu bayan samun nasara,

Manyan Mabiya Darikar Malam Ibrahim Shekarau da dama ne suka halarci taron da suka hadar da tsohon kwamishina Sarki Labaran da tsofaffin mataimaka na musamman Sabo Tafida, da Mai Koriya da Auwalu Waro Mai Zane da tsohon shugaban yan kwadago Ali Mannir da Alhaji Tasiu da tsofgin kansiloli da shugabannin rusashshiyar jamiyyar ANPP

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *