Wani kasaitaccen taron Barka da Shan Ruwa da Hadin Kan Kungiyoyin Kwallon Kafa na Jihar Kano irinsa na farko a tarihin masu kungiyoyin kwallon kafa a jihar Kano da Masu Kungiyoyin Kwallon Kafa dake Filin Mahaha suka Shirya yaja Hankalin Mahukunta da Masu Ruwa da Tsaki a Jihar Kano,
Da yake jawabi yayin taron Shugaban Hukumar Wasan Kwallon Kafa ta Jihar Kano Kuma Mamba a Hukumar Wasan Kwallon Kafa ta Kasa. Sardaunan Madakin Bichi Sharu Rabiu Ahlan yace taron abin Alfaharine ga Hukumar Wasan Kwallon Kafa ta jihar Kano Laakari da alummar da Suka halarci Taron,
Sharu Ahlan Wanda Cikin Jin dadi yace ” Nayi Mamakin Irin Tunanin Wadanda Suka Shirya Wannan Taron Kasancewar Tunanine da Zai Kawo Cigaba da Hadin Kai Tsakanin Matasa ”
” Naji dadi Kuma Sunyi Abin Ayaba Musu” inji Sharu, Wannan Abin da Sukayi Abune da Kowa Ya Kamata Yayi Koyi Dashi,
Mu ! Harkarmu ta Matasa ce Kuma Mun Gamsu da Yadda Wadannan Matasan Suka Bijiro da Wannan Tsarin Da Zai Karfafa Zumunta da Hadin Kai Tsakanin Kulab Kulab inji Sardaunan Makaman Bichi,
Da yake nasa Jawabin Shugaban Kwamitin Shirya Taron kuma Kocin Kungiyar Samba Kurna Mukhtar Abdullahi Shuaibu, ya bayyana Makasudin Taron da Cewa Tarone na Hadin Kan Kungiyoyin Kwallon Kafa, Shugabanni , Masu Horarwa da Dukkan Masu Ruwa da Tsaki a Harka,
Inda ya Kara da Cewa Lokaci Yayi Da Masu Harkar Wasan Zasu Waye Su Rungumi Juna a Duk Halin da Aka Tsinci Kai dan Haka Wasan Ke Koyarwa,
Da yake Karin Haske Kan Yadda Aka Faru Tunanin Kafa Wannan Kungiya Shugaban Kungiyar Kano Lion Coach Sa’ad Ahmad Ma,aji ( Coach Amo daga Allah ne ) Yabawa Coach Suleman Dauda Raula yayi saboda tunaninsa na kirkiro ( Group na Mahaha) da dauriyarsa na tafi da group din duk da irin kalubalen daya dinga fuskanta har jama’a suka gane amfanin sa inda a yanzu ga sakamakon daya haifar,
Daganan sai ya yabawa Shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Kano Sharu Ahlan visa Kokarinsa na jagorancin alumma bisa gaskiya,,
Shikuwa Shugaban Kingiyar Clever Warriors Dr Najib Sabo Kurawa dake zama daya daga cikin wadanda suka halarci taron, yabawa wadanda suka Shirya Taron Yayi Inda Yace Hakan Wata Alamace da Take Nuna Irin Yadda Kungiyoyin Suka Aminta da Juna inda yace ” Gaskiya na gamsu da yadda aka shirya wannan taron”
Shikuwa Maihorar da kungiyar Kano Pillars Coach Ibrahi Musa Kira Yayi ga Masu Ruwa da Taski a Harkar Wasan Kwallon Kafa a Jihar Kano dasu Zama Masu Adalci da Kaunar Juna a Tsakaninsu Tare da Taimakawa Juna a duk Lokacin da Bukatar Hakan Ta Taso,
Shima a nasa jawabin Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa A A Zaura Kuma Shugaban Shugabannin Kungiyoyin Kwallon Kafa Masoya A A Zaura na Jihar Kano Alhaji Kabiru Haruna Mahuta jan hankali yayi ga hukumomin Wasan Kwallon Kafa na Jihar Kano da Masu Kungiyoyi Yayi dasu Maida Hankali Wajen Taimakawa Matasan dake Wasan Yayi inda yace ” Ya zama wajibi masu ruwa da tsaki a harkar wasan kwallon kafa su fadada tunaninsu da gano hanyoyin da zasu tallafawa yan wasan a kowane mataki”
Sama da Shugabanni da Masu Horarwa 70 ne Suka Halarci Kasaitaccen Taron Cikin Harda Nazifi Hamidu Bako Mai Neman Takarar Zama Dan Majalisa Jiha a Karamar Hukumar Gwale,da Shugaban Kungiyar Alkalan Wasan Kwallon Kafa ta Jihar Kano da Shugaban Kungiyar Yan Jaridu Marubuta Labarin Wasanni Shiyyar Atewa Maso Yamma da Na Jihar Kano da Saura Masu Ruwa da Tsaki a Harkokin Wasan Kwallon Kafa