A yayin da gwamnatin jihar kano ke babatun bunkasa cigaban yan kasuwa da kasuwanci da habaka cigaban tattalin arziki da kasuwanci a jihar kano a waje guda ana zargin wasu daga cikin shugabannin kananan. Hukumomi.da yiwa wannan kyakyawar aniya ta gwamnati zagon kasa,
A wani abu dayayi kama da wancan abun da muka zayyana yan kasuwa a kasuwar abinci ta Dawanau bagaren yan gyada sun wayi gari da ganin wasu maaikata fa suke zargin daga karamar hukuma suke suna rushe wasu gurare da nufin yin wani aiki da zai rufe wata mahimmiyar hanya da yan kasuwar ke amfani da ita,
A tattaunawarsu da wakiliyar mu a lokacin da ta ziyarci kasuwar dan ganewa idonta abin da yan kasuwar ke kokawa Alhaji Garba A Tsoho Wakilin Kasuwar Dawanau Cewa yayin ” mun wayi gari kawai da ganin wasu maaikata sunzo sun rushe kwalbati da wasu gurare ”
Da aka tambayeshi shin ko suwaye ke wannan aiki.Alhaji tsoho cewa yayi wani mai suna ” Dan Ibadan ne yake jagorantar aikin” inda yace kuma muna zargin daga karamar hukumar Dawakin Tofa ne,
Da yake karin haske kan matsalar da suke ganin akin zai haifar dattijo Alhaji Garba A Tsoho cewa yayi “/Hanyace ake kokarin ginewa kuma ita hanyar itace ruhin bangaren yan Gyada wacce motoci ke amfani da ita wajen shige da fice kuma itace hanyar ruwa Daya tilo da kasuwar ke da ita a bangaren”
Dan gane da yadda suka kalli wannan aiki A Tsoho cewa yayi ” Cutar Adamu zaayi idan akayi wannan aikin”
Shima da yake karin haske kan irin halin da kasuwar zata tsinci kanta Abdulmalik Bala Maajin Kungiyar yan kasuwar bangaren yan gyada cewa yayi matukar aka gudanar da wannan aiki to kasuwar zata shiga wani hali da kowa zai koka laakari da matsalolin tsaro musamman idan iftilain gobara ya samu ” Allah ya kiyaye” inji Abdulmalik