Kimanin mutum Tara suka ajiye mukamansu tun bayan umarnin gwamnan.
Wani dan jarida da BBC ta tattauna dashi bashir sarki ya bayanna wadanda suka ajiye aikinsu zuwa yanzu dasuka hadarda nasir Yusuf gawuna mataimakin gwamnan kano ,wanda ya sauka daga mats a gun kwamishinan noma,da murtala sule garo, kwamishinan kananan hukumomi, da na raya karkara ,musa ilyasu kwankwaso.
Hakana shima nura Muhammad dankande kwamishinan kasafi da kwamishinan ilimi sunusi sa’idu kiru suna daga cikin wanda suka mika takardunsu na murabus.
Bashir sarki yabayyana cewa yawancin ajiye aikin nasu baya rasa nasaba da aniyarsu ta tsayawa takara, da kuma la’akari da sashen da ake ta dambarwa akansa na cikin sabuwar dokar zabe ta 2022 da ya bukaci masu Neman mukamin siyasa su ajiye aikinsu idan suna da sha’awar yin takara a yanzu .