Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A karo farko a tarihin karamar hukumar Dawakin Kudu a fagen wasan kwallon kafa, kungiyar kwallon kafa ta Jido Warriors tayi bikin bsje kolin kwafa kwafai data dauka a dan lokacin da kungiyar ta kunno kai a fagen wasan kwallon kafa a fadin jihar kano,

Kungiyar kwallon kafa ta Jido Warriors dayace daga cikin sama da kungiyoyi 100 a yakin karamar hukumar Dawakin Kudu kuma Daya daga cikin kungiyoyi sama da 10,000 a jihar kano da wannan rana ta laraba ta baje kolin kwafa kwafai 9 data samu nasarar dauka abin daya sanya ta zama kan gaba tsakanin kulab kulab dake yankin Dawakin Kudu,

A tattaunawarsa da express radio shygaban kungiyar kuma yariman Jidi wakilin Dagacin Jido Alhaji Auwalu AA Jido cewa yayi ” ya zama wajibi na godewa Allah bisa wannan nasara da lokaci daya bamu muka shirya wannan taro da duk dan asalin Jido ke fatan gani kuma ke Alfahari dashi”

A. A Jido wanda tsawon lokaci ke fadi tashi dan ganin kungiyar da garin Jido sun sami daukaka a fagen wasan kwallon kafa ya kara da cewa ” lokacine dani.kaina nake mamaki irin yadda alummar Jido ke bani goyon baya musamman manya mutane da sun girmemin a shekaru amma suke tare dani nagode”

Dayake amsa tambaya kan yadda kungiyar ta samu nasarorin tara wadannan kwafa kwafai Auwalu A A Jido cewa yayi “Ga suna ! Yan wasane da suke kishin kansu, ga hadin kai ga biyayya da kaunar juna uwa uba kuma suna kishin garin Jido to wannan shine sirrin nasarar”

Dan ganeda yadda ake tafiyar da kungiyar har takai ga wannan nasara tsohon danwasa A A Jido cewa yayi munsha gwagwarmaya da masu son su halaka kungiyar a cikin da waje amma dayake yan wasan sun sa halacci kuma suna da mutunci sun hana samun wannan barakar sun dunkule waje daya kuma sun bamu cikakken goyon baya musamnan yadda suke ” Kauna ta da Karemin Mutunci ” su da magoya baya na gida dana waje

Da yake karin haske kan yadda alummar garin Jido suka karbi kungiyar A A Jido cewa yayi ” Ba a magana, alumma garin Jido kaf na bayan kungiyar mu kuma suna nuna mana kauna ”

Dangane da sauran al amura Auwalu cewa yayi cigaban bai samu ba saida hadin kan shugabannin kungiyar wato “Officials ” nake nufi suna taka mahimmiyar rawa wajen ganin kungiyar mu tayi nasara kullum suna tare damu da bibiya da bada shawarwari cikin girmama juna da mutuntawa har muka sami wannan nasarar ” A gaskiya officials din Jido sai godiya”

Kan kalubalen dake gaban kungiyar A A cewa yayi ” lallai akwai kalu bale amma da sannu zamu cimma dukkan kalubalen,

Dayake bayyana nasarar dayafi alfahari da ita shugaban kungiyar cewa yayi nasarar da aka samu ta gasar cin kofin Hon Mustafa Bala Dawaki inda yace ” Nasarace da kowa ke alfahari da ita saboda sabon kofine dashi dan majalisa yazo dashi daga kasar waje sannan kuma duk mai ruwa da tsaki a harkar wasan kwallon kafa a jihar kano.ya halarci wasan karshe munji dadi munyi farin ciki”

Dan gane da tinja tinja data faru a kungiyar yan kwanaki cewa yayi tuni abu ya wuce sai labari

Dubban mutane ne suka halarci kasai taccen taron da suka hadarda Dagacin Malikawa da mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar kano da wakilici daga karamar hukumar Dawakin kudu da shugaban yan jaridu marubuta labarin wasanni na jihar kano da sauran alumma da yan wasa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *