A daren Lahadi ne ‘yan sanda a Kano suka yi wa gidan wani dakataccen shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC Muhuyi Magaji Rimingado kawanya.
Rahotannini na cewa ‘yan sandan sun ajiye motocinsu a kusa da gidansa na titin Yahaya Gusau, inda suka yi masa kwanton bauna da misalin karfe 7 na dare.
Mazauna yankin sun tabbatar wa DAILY NIGERIAN kawanya inda suka ce sun ji karar harbe-harbe a lokacin da ‘yan sanda ke kokarin cafke Mista Rimingado.
“Mun ji karar harbe-harbe kuma mun ga jami’an tsaro a kusa da gidan. Daga baya da misalin karfe 9:30 na dare, sai muka ji karar tayoyi yayin da suke bin wata motar da ta fito daga gidan,” in ji makwabcin Mista Rimingado wanda ya nemi a sakaya sunansa.
Sai dai babu tabbas ko ‘yan sandan sun kama shi a yayin samamen.