A yunkurinta na bunkasa cigaban wasan kwallon kafa a jihar kano, karamar hukumar Gwale da kungiyar Clever Warriors Shugaban kungiyar Dr Najib Kurawa ya bada sanarwar nada sabbin jamiai 3 dan karfafa cigaban kungiyar, a wani sako daya aikawa express radio ta shafinsa Dr Najib ya bayyana nadin Ibrahim Bawa Hassan matsayin Team Manager Sai a matsayin sabon kocin karamar kungiyar da kuma musbahu Bala Chediyar Yan Gurasa a matsayin jami’in Hulda da Jama’a.
Dr Najib ya kara cewa nadin ya biyo bayan cancantar da kowanen su yayi kan aikin sa, musamman a wannan lokacin da kungiyar ke fafafatawa a gasar ajin matasa rukuni na daya da shirye shiryen da kungiyar keyi na bunkasa cigaban yan wasa daga tushe,
Dangane da lokacin da zasu fara aiki Dr Najib cewa yayi dukkanin su zasu fara aiki nan take,
Tuni kungiyar ta fara wasanninta na bana inda tayi wasa biyu inda take da maki 3 bayan lashe wasa daya da rashin nasara daya a tsakanin kungiyoyi goma sha daya da zasu fafata gida da waje a tsakaninsu
.