Alamu masu karfi na nuni da cewa Sanata Ifeanyi Ubah, Stella Oduah, Lynda Ikpeazu, da wasu da dama na shirin ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), su koma jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Kotu ta kori gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, mataimakinsa, da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar wadanda suka sauya sheka daga PDP zuwa APC saboda sun fice daga dandalin da suka zabe su.