Kungiyar TNM karkashin jagorancin Sen. Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ta dauki jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), a matsayin dandalin siyasa domin cimma burinta na samun madafun iko a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban kwamitocin riko na jam’iyyar na kasa, AVM John Ifeimeje mai ritaya, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da shugabannin kungiyar suka gudanar a ranar Litinin a Abuja.
TNM, wanda aka kaddamar a ranar 22 ga watan Fabrairu, wata kungiya ce ta ‘yan Najeriya masu nuna damuwa da kishin kasa daga dukkan jihohin kasar nan 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja wadanda suka damu da halin da al’ummar kasar ke ciki kuma suka amince su hada kai don cin zabe a 2023.
Ifeimeje ya ce, a bisa manufofin jam’iyyar TNM, kungiyar ta kudiri aniyar hada kai, tare da daukar jam’iyyar NNPP domin ci gaba da fafutukar ceto kasar nan daga zargin tafka magudi, rashin iya aiki da rashin hukunta su, rashin tsaro da rashawa da talauci da dai sauransu.
“Don haka TNM ta hade tare da New Nigeria Peoples Party (NNPP)