Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta nuna sha’awar ta na daukar dan wasan Napoli dan asalin kasar Najeriya Victor Osimhen. Fagenwasanni.com ta rahoto.
Manchester United ta shiga kasuwa domin neman daukar dan wasan gaba a wannan kakar, Sakamakon barazanar da zata iya fuskanta na tashin Ronaldo daga kungiyar.
Masani a harkar saye da musayen ‘yan wasannin nan dan kasar Italiya, Ciro Venerato, Ya rahoto cewar Manchester United ta shiga sahun kungiyoyin da suke neman Victor Osimhen, Bayan tsohon dan wasan na Lille ya bayyana cewar zaibar kasar Italiya a karshen kakar wasa ta bana.
Dan wasan dai yazo Napoli akan kudi masu tsada, Kuma ya kafa tarihin zama dan wasan nahiyar Afrika mafi tsada da aka saya a nahiyar turai.
Kawo yanzu shugaban Napoli Aurelio De Larentiis yayiwa dan wasan darajar kudi da takai yuro miliyan 100 ga duk kungiyar da take da sha’awar daukar sa.
Kuma a bayyane yake cewar kociyan Manchester na rikon kwarya Ralf Rangnick yana kaunar dan wasan na Super Eagles.