Tsohon Dan Majalisa mai daya wakilci Kwame/Funakai jihar Gombe dake arewacin najeriya a majalisar wakilai Hon Khamis Ahmed Mailantarki yace bashi da wani buri bayan yaga ya samarwa dinbin matasa da Allah ya bawa basirar wasanni aiki a arewacin Najeriya,
A tattaunawarsa da wakilin express radio dake jihar kano cikin shirin labarin wasannin karshe mako a ranar wasan karshe nacin kofin Ramat karo na 39 da aka gudanar a kano Mailantarki cewa yayi, da mahukunta zasu maida hankali wajen bunkasa harkokin wasanni tsakanin matasa da za asha mamakin saka makon da zaa samu wajen rage aikata miyagun ayyuka tsakanin alumma,
Khamis Mailantarki wanda ya kafa kungiyar kwallon Mailantarki Sport Care yace yayi nisa wajen tunanin yadda zaa iya shawo kan matsalolin da matasa ke shiga ta hanyar bunkasa basirar da suke da ita a fagen wasanni ” Ni na gane irin matsalolin da matasa dake da basirar yin wani wasa ke gamuwa dasu matukar basu sami damar baje basirar tasu ba” inda ya kara da cewa sanin hakane yasa na bijiro da kungiyar Mailantarki Sports Care dan kulawa dasu da basu dama,,
Dayake amsa tambaya kan ko arewacin najeriya nada matasan da zasu iyayin shura a fagen wasanni tsohon Dan Majalisar Cewa Yayi ” ai arewacin najeriya sunfi kudu yan wasa masu basira idan ka dubi yadda arewr ta samar da yan wasa a baya da kuma yadda take samarwa a yanzu”
Da yake amsa tambaya kan Inko hakane meyasa yan arewa basa samun damar zuwa kasashen turai da shiga kungiyar kwallon kafa ta kasa super eagles ? sai Mailantarki yace ” To wannan shine matsalar data sani shiga cikin harkar tsundum dan na ceto matasan arewa daga wannan halin ”
Batun rashi zuwa turai da rashin samun dama a kungiyar kasa batune da yan uwammu sukayi mana nisa a ciki abin dayasa suka mamaye harkar, a kudancin najeriya masu kudi da masu Iliminsu suna zuba jari kan matasan da sukaga suna da basira kuma kome zasu kashe basa damuwa amma mu a arewa munfi yadda da kasa ka siyar dan ribs yanzu sabanin takwarorinmu,
Mailantarki wanda yace yayi tafiye tafiye kasashen turai da Amurka da Asiya dan kulla alaka da samo Ilimi na yadda zaa gudanar da kungiyar rainon yan wasa yace kawo iyanzu ya zuba jari mai tarin yawa wanda hakan wata fitilace da zata haskake arewacin najeriya nan bada dadewa ba,
Kan yadda tsarin cibiyarsa ta Mailantarki Care take Hon Khamis cewa yayi KULAWA shine CARE din kuma shiyasa muka samata suna Mailantarki Sport Care dan mu kula da matasan harsu cimma burinsu a fagen wasanni da izinin Allah,
Kan yadda matasan suka karbi kungiyar da shirin shugaban cibiyar cewa yayi ” Alhamdulillah yaran suna bada hadin kai kuma masu kula dasu suna kokari kwarai da gaske sun maidasu ya’yansu akwai girmama juna da biyayya ”
Dan gane da wasan Ramat Cup da aka kamnala inda kungiyarsa ta kare a na 3 Ahmed Mailantarki cewa yayi ” yan wasana sunyi kokari tare da nuna da a musamnam a wasan kusa da karshe mungode Allah dayasa muka gama lafiya ba rauni kuma mukayi na 3″
Shinko menene fata da burin wannan kungiyar sai shugaban yace ” Ina fatan samar da babban waje na daukar horo da karatu na yan wasan wannan cibiya ta Mailantarki kuma muna bukatar ko ya kawo matasan daga koina