Wasan kwallon kafa a Jihar Kano na bukatar taimako na musamman ta bangaren daukar nauyinsa. Fagenwasanni.com ta rahoto.
A tautaunawar mu da shugaban tsara gasar A A Zaura Cup 2022, Comrade Kabiru Haruna Mahuta (KB Mikel Mai Sallah) yace ” Idan rayuwar matasa tai kyau kuma tai ingancin bin hanya madaidaiciya tabbas kaso 85 na kyawun zaman takewa zai samu cigaba a kasa, kuma abu na farko cikin sauki da zai kawo hakan shine tallafawa harkokin wasanni, musamman kwallon kafa wadda tuni ta zama babbar sana’a a duniya.
Abin takaici yadda a Afirika ake kallon Najeriya Uwa, amma mu har yanzu yan siyasar mu da shugabannin mu basa kallon wasan kwallon kafa a matsayin babbar sana’a mai kawo makudan kudade da riba.
Kabiru Mahuta yakara da cewa ” Ina mai kira ga dukkan matasa da ku zauna da duk wani dan siyasa kuyi yarjejeniya a rubuce da alkawari idan muka zabeka to zaka dauki nauyin mu domin mu samu cigaba a bangaren Kwallon kafa domin kasashen duniya ta zamar musu hanyar samun kudaden shiga.
Kira ga shugabanni…
Kabiru Mahuta yace ” Ina rokon shugabanni da yan siyasa su sani duk yaron da suka taimakawa ya fita kasashen waje to ba shakkah samada mutane 500 ka’iya anfanuwa da cigabansa ta bangaren wasanni dama sauran al’amura.
A kano muna da matasa masu son cigaba wasan kwallon kafa Don Allah shuwagabanni a temaka musu don rayuwarsu ta inganta.