Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyar daliban Najeriya NANS, ta bayar da wa’adin mako guda ga gwamnatin tarayya, da ta warware rashin jituwar da ke tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ko kuma ta fuskanci daukar matakin gaggawa na daukacin daliban Najeriya.

NANS ta bayyana hakan lokacin da ta je Sokoto domin taronta na duba kundin tsarin mulki inda kungiyar ta duba kundin tsarin mulkinta na tsawon shekaru 40 a jami’ar Jahar Sokoto.

Shugaban NANS, Sunday Adedayo ne ya bayyana wa’adin a Sokoto jiya, bayan ya sanya hannu a kan kundin tsarin mulkin kungiyar da aka yi wa kwaskwarima a fadar gwamnatin jihar Sakoto.

Ya bayyana cewa abin takaicin halin gwamnatin tarayya da yin wasa da ASUU tun 1999 a lokacin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da kungiyar malaman.

Ya koka da yadda gwamnati ta yi watsi da harkar ilimi a matakin firamare da sakandire kuma NANS ba za ta zuba ido tana kallon yadda gwamnati ke lalata ilimin manyan makarantu ba.

Da yake jawabi tun da farko, Gwamna Tambura ya roki ASUU da su nemo hanyar warware sabanin da ke tsakaninsu ba tare da sun shiga yajin aikin ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *