Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Manyan Kungiyoyi uku na Turai sun tuntubi AC Milan ta Seria A game da zama ta hudu a gasar wasan sada zumunci. Fagenwasanni.com ta rahoto.

Real Madrid, Juventus da Barcelona suna tattaunawa kan gasar share fage na kakar wasa ta bana a Amurka, in ji wani rahoto daga ESPN.

Kungiyoyin uku suna neman sabbin hanyoyin samar da kudaden shiga bayan barkewar annobar korona kuma jerin wasannin sada zumunci a Amurka shine yunkurinsu na karshe na yin hakan bayan rashin nasarar samun kudade a gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2021.

Gayyatar AC Milan

Sun tuntubi AC Milan ta Serie A game da zama kungiya ta hudu a gasar. An yi imanin cewa gasar za ta gudana ne a gabar yammacin Amurka. An rawaito cewa garuruwa da dama na fafatawa don karbar bakuncin wasan Clasico tsakanin Madrid da Barcelona.

Kungiyoyin LaLiga sun hadu a Amurka a shekarar 2017, inda Barça ta ci 3-2 a wasan da ya kasance wasan karshe na Neymar a kungiyar kafin ya koma PSG.

Rashin nasarar kirkirar Super League

Madrid da Barcelona da kuma Juventus ne kawai kungiyoyin da har yanzu suke sha’awar samar da gasar cin kofin Super League.

Kungiyoyi goma sha biyu sun fara shiga gasar a watan Afrilun 2021. Sabuwar gasar da za ta sa su bar gasar zakarun Turai, duk da haka, Atlético Madrid, AC Milan, Inter Milan, Liverpool, Arsenal, Chelsea, Tottenham, Manchester United da Manchester City duk sun fice ne biyo bayan zanga-zangar da magoya bayan kungiyoyin Ingila da abin ya shafa suka yi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *