Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Yara dubu daya ne suka rabauta da yin shayi da a wani shirin yiwa yara shayi kyuata da shugaban karamar hukumar Tatauni Abubakar Zakari Habu P A ya bijiro dashia fadin karamar hukumar

A tattaunawarsa da manema labarai ciki harda walilin Express Radio Digital Media Salisu Musa Jegus Kansilan Maaikatar Gona na karamar hukumar Hamisu Sunusi Babannan .wanda Daya ne daga cikin rukuni biyu na masu duba aikin yace Shugaban Karamar hukumar Habu P.A ya chanchanci yabo bisa managartan tsare tsare na gudanar da shayin da abubuwan da shugaban yayi tanadin bawa ko wane yaro,

Manyan kaji biyu da Naira Dubu da magunguna kyauta,inda iyayen yaran ke ta tururuwar kai yayansu asibitin unguwa uku,

Da yake karin haske kan tanadin shugaban karamar hukumar kansilan gona Babannan cewa yayi ” Nayi mamakin yadda shugaban karamar hukumar Habu Zakari Habu P.A umarce ni da in sanar da lafiyayyaun kaji 2000 inda zaa dinga bawa kowane yaro da akayi wa shayi 2″ abinda kansilan ke cewa hakan shine irinsa na farko da wani shugaban karamar hukuma yayi wa alummarsa a tarihi,

Kwamishinan Gona na karamar hukumar Hamisu Sunusi ya kara da cewa shugaban karamar hukumar ya zama zakaran gwajin dafi a tsakanin takwarorinsa daku tarihin shygabannin karamar hukumar ta Tarauni,

Kansilan gonan wanda ya nanata nagartar shugabanci irinna shugaban karamar hukumar Habu P.A ya kara da cewa alummar karamar hukumar sunyi dacen samun shugaba daya damu da alamuransu, da cigaban karamar hukumar inda yace ya zama wajibi ya yaba masa bisa kokarinsa da sanin makamar aiki,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *