Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Duk Lokacin da aka rasa mutanen kirki a duniya babu shakkah tashin alqiyama yazo, domin babu sauran abun da ya rage.

A tautaunawar Alhaji Laminu Niger da Wakilinmu, yace yana gaida dukkan wanda wannan sako yazo gareshi kuma yanai masa fatan alkhairi. Kuma yanaso yayi amfani da wannan damar zuwa ga mutanen kwarai musamman yan kwankwasiyya na Jahar Kano dama duniya bakidaya, Yanzu lokaci yayi da babu abinda yakamata muyi illa sake dagewa da addu’oi.

Alh Laminu Niger yace “A halin yanzu babu mutanen kwarai a siyasa saboda duk sun kare kawai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya rage, bawai sai na fada muku waye Sanata Kwankwanso ba kowa yasani musamman idan kana bibiyar al’amuransa da akidunsa, kuma Insha Allahu nan gaba kadan zai shiga Villa a matsayin shugaban kasar Najeriya da Ikon Allah.

Ire-iren masu halin kwarai a siyasa irin na Sanata Rabiu Kwankwaso sun kare, Saboda Ni Alhaji Laminu Niger iya bincike wanda nayi aduniya kamar yadda na yadda da Malam Ja’afar da Albani Zaria da sauran malaman addini na kwarai, Haka na yarda da Sanata Injiniya Rabiu Musa kwankwaso a fanni siyasa, Saboda ni bawai a iya Najeriya ba a kaf Afirika ni Laminu Niger banga wanda zan’iya hadashi da Kwankwaso ba wajen lissafin siyasa.

Alh Laminu Niger yakara da cewa ga dukkan wanda yake ganin yayarda da ubangidansa to ya gayyaceni muzauna dashi domin mutautauna akan halayensu da sauransu.

A lokacin dana taso girma, idan naga dan siyasa yana magana da sauransu sai ince karya ce, cutane suna cin mulki shikenan babu ruwansu da kowa, To amma dana shigo harkar Sanata Rabiu musa Kwankwanso, kuma kafin inbishi saida nafara duban irin maganganun da yakeyi sannan nayi bincike iyakar iyawata na tabbatar lailai a rayuwa karkaga kowa yanayin badaidai ba ka daukesu duk daya ne ko kowa haka yake, kamar yadda idan mutanen kirki suka kare to ranar ne Allah zai tashi duniya kowa ya mutu.

A fanni Siyasa yanzu maganar da ake babu wani dan siyasa samada Rabiu Musa Kwankwaso, kuma duk dan siyasar da zaiyi magana tsakani da Allah zai fadi kyawawan halinsa domin a yanzu kamarsa ko irinsa babushi, Saidai irin yaransa da matasa da suke tafiyarsa suke koyon halinsa to ba shakka muna musu fatan anan gaba zasu kasance kamarsa musamman idan sun dora a layin da yake nunawa.

Babban abin dubawa shine, indai yau mutum yana kan mulki kuma zaina dubawa yaga wanne yankine ko gurine mutanen gun suke shan wahala bari mu taimaka musu mu kawo musu mafita da sauki cikin alamuransu to irin wannan shugaban yagama komai a duniya.

Daga karshe Alhaji Laminu Niger yayi godiya ga ilahirin masoyansa dana kwankwansiyya da mawaka masu rera masa wakoki, tare da yin godiya ta musamman ga masoyansa da yi musu fatan alkahiri a duk inda suke Allah ya ingantar da rasuwarsu ameen.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *