Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea takara matsawa gaba a wajen neman dan wasan bayan Real Madrid Eder Militao. Fagenwasanni.com ta rahoto.

Jaridar Marca tace dan wasan baya na tsakiyar mai shekaru 24 yana da ragowar kwantaragi da Real Madrid har na tsawon shekaru uku.

Amma kuma yana daya daga cikin ‘yan wasan da suke karbar mafi karancin Albashi a kungiyar da Albashin yuro miliyan 2.5.

A bayyane yake cewar Real Madrid naso dan wasan ya cigaba da zama a kungiyar, Amma kawo yanzu babu wata sabuwar tattaunawa da sukayi a tebur.

Amma abangaren dan wasan shima a bayyane yake cewar bayason barin kungiyar, Saboda yana jin dadin aiki a karkashin Carlos Ancelloti.

Saidai duk da haka dan wasan na kasar Brazil yana samun kira daga kungiyoyi da dama a nahiyar turai, Ciki harda Bayern Munich.

Amma ahalin yanzu Chelsea na tunanin kara matsa kaimi akan dan wasan kuma ta fara tattaunawa da wakilin sa domin yiyuwar komawar sa Stamford Brigde da fafata wasa.

 

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *