Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ernesto Valverde, Yana samun kira daga Atletico Madrid domin ya maye gurbin mai horas wa Diego Simeone. Fagenwasanni.com ta rahoto.

Ahalin yanzu dai Diego Simeone yana fuskantar matsin lamba a kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Bayan rashin kokari da kungiyar take agasar Laliga.

Sannan kuma kungiyar zata kara da Manchester United agasar zakarun nahiyar turai matakin zagaye na’yan 16 a sati mai zuwa.

Jaridar Sport tace shugaban tsare-tsaren kungiyar ta Atletico Madrid yace a yanzu mai horas war na Argentina yana cikin kariyar su bashi da wata matsala saidai idan shine yaso rabuwa dasu akaran kansa sakamakon abunda ya bawa kungiyar acikin shekaru 10 da suka gabata.

Shin ko Simeone zai iya zabar barin Atletico Madrid a kakar wasa ta bana – Da wurwuri – Amma kuma Atletico Madrid ta sanya Valverde acikin jerin wadanda zasu maye gurbin mai horas war idan har ya zabi barin kungiyar.

Diego Simeone yana da ragowar kwantaragi da Atletico Madrid har zuwa shekarar 2024.

Daga Aliyu Alhassan Falgore

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *