Tsohon dan majalisar tarayya daya wakilci Kwame/Funakai a jihar Gombe kuma shugaban kungiyar rainon yan wasan kwallon kafa ta Mailantarki Sports Academy Khamis Ahmed Mailantarki yace jihar na da wani arziki da zai bunkasa cigaban tattalin arziki da samar da Ayyukan yi ga matasa da bata kallon sa,
A wata tattaunawa da Khamis Mailantarki yayi da manema labarai ciki harda wakilin Express Radio Salisu Musa Jegus a lokacin da ake gudanar da wasan cin kofin Ramat Karo na 39 a kano Khamis yace yayi mamakin ganin katafaren filin wasanni na MAHAHA SPORT COMPLEX dake ungiwar Kofar Naisa kan titin jamiar Bayero, abin da mai lantarkin ke cewa ” Wannan filin shi kadai zai bawa matasa sama da 500,000 aikin yi da zasu dogara da kansu idan akayi amfani dashi yadda ya dace “amma abin mamakin shine yadda yaga anyi watsi da filayen da aka samar wadanda in a kudancin kasarnan ne da ansha mamaki inji Mailantarki
Mailantarki wanda ya kafa kungiyar rainon matasan yan wasan kwallon kafa a jihar Gombe irinta ta farko a arewacin da nufin samarwa da matasa kyakykywar makoma da bunkasa basirar da suke da ita a fagen wasanni, ya cika da mamakin yadda yaga matasa a jihar kano dake da son wasanni da matasan masu horar da wasa da shugabanni dake da buri kan wasan kwallon kafa amma basu sami cikakken goyon baya daga mahukuntaba abin da Mailantarkin ke cewa shiya sanya koma bayan da kungiyoyin ke samu,
Da yake tsokaci kan yadda ya kamata gwamnatin jihar kano tayi da dinbin mstasa dake son yin wasanni a matsayin sana’a a jihar kano Shugaban kungiyar Mailantarki Sport cewa yayi da ! Gwamnatin jihar kano zata inganta filin wasa na Mahaha tare da gina wasu filaye a unguwanni da garururwa da taga yadda wasan zai samar da matasan da zasu zama wani abu ba a jihar ko kasa ko afrika ba harma a duniya,
Mailantarki wanda ya bada misali da Ahmed Musa yace akwai irin Ahmed sama da 1000 a jihar kano amma rashin kulawar mahukunta bai bssu damar fito da kansu ba, ” Da zaa shiga cikin alamuransu da anga abin mamaki ” inji tsohon dan majalisar,
Da yake amsa tambaya kan yadda ya tsunduma harkokin wasanni duk da irin dinbin ayyukan dake gabansa Khamis Ahmed cewa yayi hakan ya zama dole a gareshi laakari da yadda matasa suka nuna masa halacci lokacin da yayi takarrar majalisa wakilai a Gombe a jamiyyar Adawa kuma ya lashe zaben da gagarumin rinjaye da yafi na kowane dan majalisa,
Mailantarki ya kara da cewa laakari da yadda ya fuskanci halin da matasa ke ciki na bukatar samum abinyi musamman yadda suke bin harkokin wasanni kuma musamman kwallon kafa sai ya yanke hukuncin shiga dan talkafawa matasan cimma burinsu wanda kawo iyanzu kungiyarsa ta MAILANTARKI SPORT ACADEMY ta kulla alaka da wasu manyan kungiyoyi kwallon kafa a kasashen turai kamar Ingila da Portugal da wasa kasashe inda kawo iyanzu wasu yan wasan kungiyar ke can suna taka leda,
Dan gane da kalubalen da wasan ke fuskanta a arewcin najeriya Malantarki cewa yayi samar da ingantattun filayen wasan shine na farko kuma ” ni na shiryawa hakan muna gina filin wasa da zai gogayya da kowane fili wajen rainon yan wasa