Ana dab da fara babbar gasar nan mai suna A A Zaura Gwamnan Kano 2023, wadda shugaban kamfanin Mahuta Ventures Comrade Kabiru Haruna Mahuta yake shiryawa. Fagenwasanni.com ta rahoto.
A wani taron bayarda tallafi wanda Kabiru Mahuta ya shirya don taimakawa daliban makarantar firemaren Gaida da Maganguna karkashin Kamfaninsa na Mahuta da kuma Gidauniyar A A Zaura Football Cup 2022, yace ” Kwallon kafa tafi komai saurin kawo zaman lafiya da soyayya tare da habbaka cigaban matasa, hakan yasa muketa kokarin ganin mun sanya babbar gasa wadda ba’a tabayin kamarta ba a Jahar Kano.
Mun sanya sunan wannan Gasa A A Zaura Cup 2022 saboda irin taimakonsa ga bayin Allah, musamman matasa, Sau da yawa matasa sunata kiraye-kirayen yakamata yan siyasa su shigo harkokin wasanni amma abin shuru ko yaushe, mu yanzu mun shigo kuma insha Allahu A A Zaura zai taimakawa matasan jihar Kano a bangaren wasanni a dalilin mu.
Yaya kuka tsara wannan Gasar?
Wannan gasar zamu gudanar da ita ga Kungiyoyin Kananan hukumomin Jahar Kano, kuma zamu zabo wadansu kungiyoyi daga Kananan hukumoni amma wadanda keda Rajista da Hukumar kwallon kafa ta Jahar Kano.
Duk kungiyar da take son ta ganta a cikin wannan gasar dole sai tana da rajista da hukumar kwallon kafa ta Jahar Kano (K.S.F.A). Saboda gasar zata kasance da manyan dokoki da tsari mai kyau, ta yadda duk kungiyar data bamu matsala zamuyi kararta ga hukumar kwallon kafa ta Kano.
Kabiru Mahuta yakara dace ” Irin wannan gasar muka rasa a Jahar Kano domin taimakawa wasan kwallon kafa, kuma tabbas zamu sanya manyan kyaututtuka wadanda zasu kara jan hankalin mahukunta daga makwabtan jihohin Kano gabadaya bama iya jahar Kano ba.
Daga karshe ya roki dukkan mahukunta da masu ruwa da tsaki a bangaren kwallon kafa da su kasance ko yaushe masu kara wayarwa da yaransu kai a game da alfanun wasan kwallon kafa.