Shugaban hukumar yaki da masu sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai murabus ya bukaci jami’o’in kasar da su bullo da tsarin yi wa dalibai gwajin miyagun kwayoyi domin raba matasa da ta’ada.
Ya nemi jami’o’in kasar da su sa tsarin gwajin amfani da miyagun kewayoyin a kan sabbi da kuma tsaffin daliban da ke karatu a cikinsu ya da zama cikin manufofinsu.
Janar Marwa wanda ya bukaci hakan a yayin kaddamar da gangamin yaki da miyagun kwayoyi a jami’o’i, a ranar Laraba, a bikin da aka gudanar a Jami’ar Abuja, ya kuma nemi hadin kansu domin kafa kananan ofisoshin hukumar a makarantu domin taimaka musu a yaki da miyagun kwayoyi.
Marwa ya ce bullo da tsarin gwajin kwayoyin a kan dalibai ba yana nufin wani mataki na hukunta su ba ne, illa dai kawai ya zama wata hanya ta gano masu amfani da kwayoyin da wuri domin dakile matsalar tun daga tushe da yi musu magani.
Shugaban na NDLEA ya ce babu wani lokaci da ya wuce yanzu da ya kamata a tashi tsaye domin maganin matsalar ta amfani da miyagun kwayoyi saboda ta’adda ce da ta zama babban abun damuwa a kasa.