Hukumar kwallon kafa ta kasa, NFF ta sanar da sauya fasalin yadda Tawagar kasar, Super Eagles za ta kasance.
NFF tace mai rikon kwaryan kungiyar Augustine Eguavoen zai ci gaba da aikin da yake kai, yayin da tsohon dan wasan Eagles din Emmanuel Amuneke zai zame masa mataimaki.
A sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun sakatare janar nata Dr Muhammad Sanusi, tace hukumar ta amince Augustine Eguavon yaci gaba da horar da Super Eagles a matsayin kocin riko, yayin da Emmanuel Amuneke zai yi masa mataimaki.
Har ilayau tace tsohon dan wasan bayan kungiyar Joseph Yobo da Salisu Yusuf zasu ci gaba da kasancewa a matsayin mataimaka a kungiyar.
Amuneke yayi aiki da NFF a baya a matsayin kocin karamar kungiya ta ‘yan-kasa da shekara 20.
Sanarwar ta kuma bayyana karara cewa ta dakatar da yarjejeniyar da ta tsara kullawa da Jose Peseiro, wanda aka sa ran cewa zai karbi aiki daga Eguavoen da zarar an kammala gasar cin kofin nahiyar Afrika.
Emmanuel Amuneke ya ta’ba jagorantar Tawagar kasar Tanzania a gasar AFCON a 2019, ya kuma kasance mamba a kwamitin bincike da nazari na hukumar kwallon kafa ta duniya da data Afirka CAF.
NFF ba ta fito ta bayyana dalilin fasa dauko mai horarwa ba daga kasashen waje, to amma ana ganin sauye-sauyen da ta bullo da su, baya rasa nasaba da kasa tabuka abin a-zo-a-gani da Super Eagles ta yi a gasar AFCON da aka kammala ranar Lahadi a Kamaru, wadda Senegal ta yi nasara daukar kofin a wasan karshe da Masar.
A wata mai zuwa ne Najeriya za ta kara da Ghana gida da waje, a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar cikin watan Nuwamba.