Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Kwallon kafa Masoya Abdussalam Abdulkari A A Zaura na jihar Kano Kuma Shugaban Kamfanin Mahuta Ventures Kabiru Haruna Mahuta yace samun mutum irin A A Zaura wata baiwace da Allah zai yiwa matasan Kano Masu Harkokin Wasanni,

A wata hira ta musamnan da yayi da express radio online Kabiru Mahuta yace ya Dade yana bibiyar irin ayyuka da A A Zaura keyi na tallafawa alumma, gine gine taimakawa gwamnati a wasu abubuwa, da dalilan da ya sanyashi yin hakan inda Kabiru Mahutan yace daga karshe ya gano cewa taimakawa mutane a jinin. A A Zaura ne kawai badan yana Neman wani Abu ko mukami ba,

Da yake amsa tambaya kan dalilin yasa ya fadi haka sai shugaban kamfanin na Mahuta Ventures yace ” yau da nake wannan hirar dakai shekara ta bakwai kenan bin diddigin yadda A A Zaura ke taimakon alumma tun kafin ya fito Neman takara a zaben Daya gabata na 2019 bai gajiya ba” kuma da Dan takarar kawai yakeyi ai saiya tsaya sai lokacin bukata yayi sannan ya fito kamar yadda wasu yan taka kara sukeyi inji Kabiru Mahuta,

Dan gane da yadda ake bada nasa taimakon da sunan A A Zaura shugaban kungiyar Gaida United cewa yayi ” yiwa Wanda kake kauna hidima ba tare daya sani ba ko ya sanka ba shine kauna ta gaskiya” bata ganin ido ba,

Ko a yan kwanakin nan mun tsikayo Kabiru Mahuta a wata makarantar firamare ta Gaida Special inda ya kai musu tallafin Kayan koyo da koyarwa da magunguna da sunan A A Zaura kayan da shugabar makarantar tace zasu taimaka matuka gaya wajen cigaban makarantar,

Haka kuma mun gana dashi a wani gagarumin taro daya shirya dan tallafawa kungiyoyin kwallon kafa guda Dari 100 inda ya basu kwallaye da kayan atisaye,

Da muka tambayeshi ko akwai wata dangantaka ta kud da kud da yake da ita da A A Zaura ? Shugaban na Mahuta Ventures cewa yayi ” ko kadan banma taba ganinsa ido da ido ba sai a wannan lokacin daya nemeni”

To Inko hakane meyasa kake bada wadancan tallafi da sunansa sai Kabiru Mahuta cikin fara’a yace ” kai dan jarida soyayya halak ce, ina kaunar A A Zaura saboda yadda na gane yana kaunar alumma kamar yadda nima nake kaunarsu hakanne yasani in taimaki mutane da sunansa inda bai kai ba ”

” Wakilcin mutumin kirki dai dai ne kuma ina son in kare masa wani wajen da bai gani ba ni zan ganar masa kuma zan kare masa wajen ” fatana alummar jihar kano su fahimci A A Zaura su gane cewa shugabancinsa inshaallahu zai zama alheri ga alumma musamman mata da matasa inji Kabiru Mahuta

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *