Sergio Ramos dai ya shafe kusan watanni 12 da suka gabata yana fafutukar samun sauki kuma a yanzu ana fargabar cewa fitaccen dan wasan bayan na kasar Sipaniya ka’iya yin ritaya da wuri saboda raunin da yake fama da shi. Fagenwasanni.com ta rahoto.
Ramos dai ya samu nasarar buga wa Paris Saint-Germain wasanni biyar ne tun bayan da ya koma Real Madrid a bara, inda ya shafe mintuna 90 sau biyu kacal.
Dan wasan bayan, wanda zai cika shekara 36 a wata mai zuwa, a halin yanzu yana murmurewa daga raunin da ya ji, kuma ana sa ran ba zai buga wasan farko na zagaye na 16 na gasar zakarun Turai da tsohuwar kungiyarsa ta Real ranar 15 ga watan Fabrairu, yayin da kuma zai yi cigaba da fama da rashin lafiya. Saidai ana tunanin ka’iya buga karawa ta biyu a Santiago Bernabeu.
Kuma a cewar wani rahoto a jaridar Le Parisien, akwai fargabar cewa za a tilastawa Ramos ya rataya takalminsa tun da wuri fiye da yadda aka tsara shi saboda matsalar raunin da yake fama da shi.: