Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar tattara bayanan sirri kan kudade ta bankado masu daukar nauyin masu ta’addanci kimanin 96 da masu alaka da kamfanonin hada-hadar kudi 424.

Ministan yada lanarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan, a yayin wani bayani da ya yi kan yaki da cin hanci da gwamnatin shugaba Buhari ta sanya a gaba.

Ya kara da cewa an gano kamfanoni 123 da wasu kananan kanfanoni 33 na masu musayar kudi da ke da alaka da ‘yan ta’adda a kasar.

Yace, A bayanan rahotan bangarenta, a sharhin da ta yi kan kudade na 2020-2021, ta bayyana masu hada-hadar kudaden 96 da ke da alaka da ‘yan ta’addan a kasar da kuma wasu 424 da ke samar da kudade domin ta’addanci da suka hadar da kamfanoni 123, da kuma na masu musayar kudi 33.

Kazalika an gano karin wasu 26 da ake zargi da ta’addanci da wasu 7 da ake hada kai da su kan harkokin ta’addanci. Wannan bayani ya kai ga kama 45 da ake zargi wadanda kwanan nan za a gabatar da su a gaban kuliya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *