A cewar bayanai da aka tattaro, an sace mutane shida yayin harin da aka kai a gidan shugaban ASUU na Damba Quaters, a wajen Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Wani ma`aikacin jami`ar kuma dan uwan shugaban na ASUU ya shaida cewa yan bindigan sun afka gidan Adamu ne a safiyar yau Laraba sannan suka sace mutane biyar.
Masu garkuwar sun sace wani makwabci, wanda shima ma`aikaci ne a sashin kula da biyan kudade na jami`ar.
Majiyar ta kara da cewa shugaban na ASUU bai kwana a gida ba a jiya Talata, don haka baya nan a lokacin da aka kai harin.
Wadanda aka sace a gidan shugaban ASUUn sun hada da kaninsa, yar kaninsa, dan kaninsa da kannen matansa biyu.