Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

Cikakken magoyin bayan kungiya shine wanda ke bin kungiyar har inda take fafata wasanta, Kano Pillars tana da dumbin masoya a duniya. Fagenwasanni.com ta rahoto.

A tautaunawar wakilinmu da wani cikakken magoyin bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano wato Wakil Mamman Ngelzarma wanda haifaffen garin Jahar Yobe ne karamar hukumar Fune, ya bayyana irin yadda yake matukar kaunar Kano Pillars a cikin zuciyarsa.

Wakil Mamman yace ” Ni masoyin Kano Pillars ne na tsahon shekaru, tun a shekarar 2006 nafara son kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Ganin yadda suke taka leda a wasannin su nagida dana nahiyar Afirika. Nakanyi tattaki naje har garin kano domin kallon wasannin kano pillars nagida alokacin da suke taka wasansu na gida a garin kano.

Saidai a yanzu abunda yake Cimin tuwo a kwarya ayanzu akan Kano Pillars shine rashin fafata wasanninsu nagida agarin kano, Wannan yana daya daga cikin abunda yake kawo mana matsalar rashin yawan jefa kwallo a raga.

Sannan ina kira ga gomnatin jahar kano Karkashin Jagorancin Maigirma Gomna Dr Abdullahi Umar Ganduje akan Gomnati tashiga wannan lamari kanin ganin angyara ciyawar da take cikin filin, Domin ansa sabuwa inaso naga mundawo fafata wasa agarin kano.

Sannan matsalar ta biyu shine inaso duk wani masoyin Kano Pillars yaci gaba da karawa masu horar da kungiyar Karkashin Jagorancin Salisu Yusuf da Ibrahim A Musa karfin gwiwa bawai adinga shiga kafar yada labarai ana zaginsu ba. Duk masoyin Masu Gida na asali Bazai kushe wakilcinsu ba. Kuma bazai so yaga babbar kungiya a nahiyar africa kamar wannan tana yawan canja masu horarwar ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *