Lashe kofi ba sabon abubane ga kungiyar Jido warriors kungiyar da tayi zarra tsakanin takwarorinta dake yankin karamar hukumar dawakin kudu dubada irin tarin nasarori da ta samu a wasanni makamanta wannan.
A ranar lahadi ne kungiyar ta Jido Warriors karkashin Jagorancin Alhaji Auwalu A.A Jido ta kafa sabon tarihin lashe sabon kofin da wakilin kananan hukumomin dawakin kudu da warawa Hon Mustafa Bala Dawaki ya sanya,
Wasan karshen da aka fafata tsakaninta da Kungiyar kwallon kafa ta garin gano,an tashi Jido Warriors nada ci 2-0 bayan tatamurza da kai ruwa rana da akayi tsakanin kungiyoyin da suka baje kolin basira da taka leda mai kayatarwar gaske,
Auwalu A A Jido Jagoran kungiyar a tattaunawarsa da express radio online ya bayyana nasarar da cewa ” Wani sabon babine da kungiyar zata bude a sabuwar shekara ta 2022″ inda ya kara da cewa kungiyar zata saka sabon dan ba na tunkarar dukkanin kalubale na cikin gida da waje dan ganin ta cimma nasarori da ta sanya a gaba,
Da yake amsa tambaya kan yadda ake kallon kungiyar a yankin karamar hukumar dawakin kudu AA Jido cewa yayi ” kan yan kungiyar mu a hade yake babu wata baraka a tsakaninmu ” duk masu kallon kungiyar da wani abu to ina sanar dasu cewa kungiyar mu tananan lafiya kuma kowa ya gani babu wani sabani a tsakaninmu a jiya,
F
Dan ganene da shirin da shugaban ke cewa kungiyar zatayi a bana Jido Cewa yayi ” zamuzo da kyawawan tsare tsare da zasu kara karfin gwiywar yan wasa da yan kallon mu fiye dana baya inji Auwalu AA ,
Dayake bayyana farin cikinsa kan daukar sabon kofin da kungiyar ya dauka Auwalu A A cewa yayi abin farin ciki shine daukar kofin dayafi kowane kofi darajar kudi da aka taba sawa ba a Dawakin Kudu ba a jihar kano baki daya, hakan abin Alfaharine da jin dadi ” Naji dadi kuma yan wasa da masu horarwa sun birgeni sun fitar damu kunya nagode musu kwarai”
A kwanakin baya wasu rahotanni da bamu tabbatar dasuba na cewa kungiyar ta samu rikicin cikin gida, abin da ya nemi zubar da kima da kwarjinin da kungiyar ke dashi a Idon masana harkokin wasanni a jihar kano,