Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gidauniyar KDC Foundation dake nan Kano, tace yanzu haka ta ware makarantun tsangayu 60 daga wasu jahohin arewacin kasar nan domin fara gwada amfani da manhajar tsarin karatu a tsangayu.

Acewar gidauniyar wannan na daga cikin ko karin da sukeyi domin kawo karshen matsalolin da makarantun da malamansu ke fuskanta.

Wakilinmu Muhammad Adam T/Murtala na daga cikin mahalarta taron ga rahoton daya hada mana.

Shugaban gidauniyar Khalifa Musatapha Dan Kade, ya bayyana cewa cikin jahohi 6n su waro makarantu 10-10ne domin fara gwada tasirin manhajar.

Khalifa Dankade, na wannan jawaban ne lokacin da gidauniyar ta shirya wani taron masu ruwa da tsaki kan makarantu tsangaya da suka hadar da Malaman tsangayu na ainahin, da jami’an gwamnati, da iyayen Yara da kuma Yan jaridu domin tabbatar da cewa ba abar wani gibi a Shirin fara amfani da manhajar a makarantunbtsangayun.

Wasu daga cikin malaman tsangayun da wakilinmu Muhammad Adam Tudun Murtala ya samu ji daga bakunannsu, sun ce a shirye suke su dabbaka wannan tsari domin zamanantar da tsarin karatunsu.

Sun Kara da cewa tsarin zai iya dorewa ne idan har an inganta makarantun ta hanyar samar da fine fine a makarantar, kamar dakunan Kwana, da ban dakuna da kuma dakunan karatu.

Makarantun tsangayu na daga cikin muhimman bangarorin dake fuskantar tarin kalu bale musamman anan Nigeria, la’akari da yadda gwamnati da al’umma basa taimakawa bangaran yadda ya kamata duk ko da irin yadda tsarin ke Shan suka daga wasu bangarorin al’umma.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *